Matan kirki
Kalmar *"MACE"* tamkar *GOLD* ne
ko kuma muce Sinadarin *ZINARI* mai yin *WALKIYA* a kowane *LOKACI*
*MATA*
Sunada wani *SINADARI*na *FARIN JINI* wanda yake da matukar Tasiri ga idon *MAZAJE*
*MATA*
Sunada matukar kima a Cikin
Al'Ummah wadda har takai ga
sun samu martaba da matsayi Babbah.
*MATA*
Sunada wani *LAUNI* mai Juya *MAZAJE* Tamkar Limzamin *DOKI*
komai *MATSAYINKA* *MULKI, KUƊI* ko *SARAUTA MACE* sai ta Juya ka.
*MATA*
Sun Amsa Sunan Su *MATA* ga jan
*AJI*
da Juyin Juya Hali, komai Rashin Kyan *MACE* Kalma daya Zata sa *KASO* ta nan Take.
*MATA*
Sunada Hikima da Jurewa akan
abunda suke matukar *SO* amman sai sukasa Nunawa.
*MATA*
Sunada Kunya, Hakuri da Juriya har sukan burgeka idan Ka Iya Zama
Dasu.
*MATA*
Basu son mai kuntata masu koda
yaushe sunfi son Mai kyauta ta masu.
*MATA*
Suna son *RAHA* da Abun *DARIYA*
ko kuma Nishadantarwa.
*MATA*
Zuciyar su *FARA* ce tamkar farin
*RUWA* ba wuya shawo kansu idan
ransu ya Baci.
*MATA*
Sunada *HAKURI* da Tausayi da kuma Firgita akan wani abu Kadan.
*MATA*
Basa son, Saunan Mutum ko kuma ƙazamin Mutum.
*MATA*
Sunfi son mai *BASU* ako wane Lokaci da kuma nuna Tausayi agare *SU.*
*MATA*
Suna jajir cewa akan nuna *SOYAYYA* da Tausayin Junan.
*MATA*
Sunfi son mutum mai *HAKURI* da
zafin naima har sukan yin Alfahari da Wannan.
*MATA*
Sunada Yauqi da son *DAULA* da kuma Anunasu Manya ne.
*DARAJOJIN MATA GUDA (16) DA SUKA ƊARA MAZA! (USIKUM FIN NISA'I KAIRA)*
Inai muku wasicci da Alkairi ga
mata "Inji Manzon Allah {s.a.w} a cikin Huɗubar Ban Kwana"
*1- MACE CE*
*TA FARA MUSULUNTA* a duk
duniya kuma ta yiwa musulunci hidima da dukiyar ta da duk abinda ta mallaka harda GwalaGwalanta *(NANA KHADIJA) (R.A)*
*2- MACE CE*
Farkon wanda ta fara Istimbabi a cikin shari'ar musulunci........
*(NANA KHADIJA) (R.A)*
*3- MACE CE*
Sanadiyyar samun Taimama a shari'a *(UMMUNA A'ISHA) R.A*
*4- MACE CE*
Ta ilmantar da Sahabbai bayan wafatin Annabi{s.a.w}
*NANA A'ISHA (R.a)*
*5- MACE CE*
Sanadiyar tsiran sahabbai daga fushin Allah sanda akai sulhun
*HUDAIBIYYA* Kuma *MACE* ce ta shawo akan *SAHABBAI* har suka tsira daga fushin Allah.
*(UMMU SALAMA) R.A*
*6- MACE CE*
Ta Kwantarwa Manzon Allah *HANKALI* Lokacin da Ifk ya faru a madina, kafin saukar wahayi
*(BARIRA) (R.A)*
*7- MACE CE*
Wanda Manzon Allah *{S.A.W}* yace idan mutum ya tarbiyyantar da
ita koda bashi ya haife ta ba, zai shiga *ALJANNA* shi da Manzon Allah *{S.A.W}*
*8- MACE CE*
Ta zamo Ma'auni damai Aure zai gwada kimarsa agun Mahaliccinsa, idan ya kyautata mata yanada sakamako mai kyau, idan kuma ya cuceta akwai uquba daga Allah.
*9- MACE CE*
Shari'a ta tanadar *MATA* Ladan Jam'im Salloli guda biyar (5)
Da Juma'a da Jana'iza da Jihadi
duk basai taje ba,amma sanadiyyar ta Kyautatawa *MIJINTA* Allah Zai bata duk *LADAN* wadannan Ibadun.
*10- MACE CE*
Sanadiyyar warware matsalar Zihari, suratul *(MUJADALA)*
*11- MACE CE*
Ta fara yin Sa'ayi tsakanin *SAFA da MARWA (HAJARA)*
*12- MACE CE*
Sanadiyyar tsiran mutanen sarauniyar Saba, suratl *(NAML)*
*BILKISU MAI GADON ZINARI*
*13- MACE CE*
Sanadiyar musuluntar Sayyiduna Umar *(R.A) (FATIMA)*
*14-,MACE CE*
Ake samun nutsuwa da ita! *LITASKUNU ILAIHA* Namiji bazai taba samun sukuni ba sai yana da mace!
*15- MACE CE*
Duk mulkin mutum da dukiyar shi sai da ita yake kara kima a idon mutane! godiya nake.
*Mata iyayen mune Mugirmamasu!*
Well
ReplyDelete