Saturday, August 11, 2018

Labarin soyayya

LABARIN SOYAYYA


LABARIN SOYAYYA

Soyayyar Annabina nake nufin in gaya muku, ba soyayyar wani ko Wata ba...


TSANTSAR SOYAYYA : ita ce lokacin da Masu kudi da dukiya suka fito suna son Nana Khadeeja (ra) amma ta Qisu tace ita MUHAMMADUR RASULULLAHI takeso.

kuma bayan ta aureshi sai ta hakura da komai na duniya.. Ta zama ita ce Khadimar Ma'aiki (saww) ta farko tun kafin Annabta..

Ta mallaka masa dukkan Miliyoyin dukiyarta...


TSANTSAR SOYAYYA : Ita ce lokacin da Sayyuduna Zaidu bn Harithata (ra) 'Yan uwansa suka zo domin su fansheshi daga bauta, Sai yace musu A'a shi ya gwammaci ya zauna amatsayin bawa awajen  Manzon Allah (saww) maimakon ya koma garinsu.

TSANTSAR SOYAYYA : Ita ce lokacin da Manzon Allah (saww)  yasha ruwa daga cikin wata Gora agidan Ummu Sulaym (ra)  sai ita Ummu Sulaim din ta tashi ta yanke bakin gorar daidai wajen da bakin Manzon Allah (saww) mai daraja ya ta'ba, ta ajiyeshi domin neman albarkarsa (SAWW).


TSANTSAR SOYAYYA : ita ce lokacin da Abu Turab Wato Shugaban Sadaukai, Imam Aliyu Bn Abi Talib (rta) ya yarda ya amince ya kwanta akan Shimfidar Ma'aiki (saww) acikin daren da Mushrikai suke nufin su kasheshi..

Ya yarda ya kwanta amadadinsa, duk da yasan cewa zasu iya harbinsa da kibiya ko su kasheshi tun kafin su gane cewa ba Ma'aikin bane awajen. (saww)


TSANTSAR SOYAYYA ITA CE : Lokacin da Bilal Al-Habashiy ya dena kiran sallah tun daga ranar da Ma'aiki ya bar duniya!!

Bilalu (rta) bai Qara yin kiran sallah ba... Sai rannan Sayyiduna Umar (ra) yace masa yazo yayi (aranar da aka karbo Masallacin Qudus).

Da Bilalu ya fara kiran sallah, yazo daidai wajen "ASH-HADU ANNA MUHAMMADAR RASULULLAH!! Yana fada haka, sai ya fashe da kuka, Sahabbai ma kowa sai kuka...

An ce ba'a ta'ba ganin ranar da daruruwan Sahabbai sukayi kuka suka zubar da hawayesosai kamar wannan ranar ba... Sai sukaji Tamkar awannan lokacin ne Ma'aiki ya bar duniya!!


TSANTSAR SOYAYYA : Ita ce lokacin da Manzon Allah (saww) yazo gidan Sayyiduna Abubakrin (ra) yace masa "ALLAH YA UMURCENI INYI HIJIRA".

Sai Sayyiduna Abubakar yace "Ina fatan tare dani zaka tafi?" Sai Ma'aiki yace masa "KWARAI KUWA. ALLAH YACE MUN IN TAFI TARE DAKAI".

Sai Sayyiduna Abubakar ya fashe da kuka don murna!!! Allahu Akbar!!!


TSANTSAR SOYAYYA : Ita ce lokacin da Manzon Allah (saww) ya kwanta barci akan cinyar Sayyiduna Abubakar (ra) alokacin da suke cikin Kogo.. Sai Sayyiduna Abubakar ya rika yagar rigarsa yana tottoshe ramukan da suke cikin kogon. Amma duk da haka akwai sauran wani rami wanda bai samu abin tosheshi ba.

Chan sai ga wani Maciji ya leko ta cikin wannan ramin yana so zai fito. Don haka sai Sayyiduna Abubakar ya sanya Qafarsa ya toshe ramin don kar Macijin nan ya fito ya chutar da Manzon Allah (saww).

Macijin nan yayi ta cizonsa yana zuba masa dafi. Amma duk da haka bai motsa ba, don kar ya tashi Manzon Allah (saww).


TSANTSAR SOYAYYA : Ita ce lokacin da Manzon Allah (saww) ya tambayi Khadiminsa wato Sayyiduna Rabee'atu bn Ka'ab (ra) : "MECECE BUKATARKA?".

Sai yace : "MAKOBTAKA DA KAI NAKE SO AGIDAN ALJANNAH".

TSANTSAR SOYAYYA : Ita ce lokacin da wata Mata Mijinta da Mahaifinta da 'Dan uwanta duk suka yi shahada awajen Yaqin Uhudu, Mutane suna yi mata Ta'aziyyah amma bata sauraresu ba..

Ita dai tana tambayar yaya Manzon Allah (saww) yake??  Da aka kaita wajensa, ta ganshi sai tace : "DUK WATA MUSIBAH AI QANKANUWA CE BAYAN KAI YA RASULALLAHI!! (Wato rashinka shine Babban Musiba. Amma tunda kana nan da ranka, to babu damuwa Ya Ma'aikin Allah!!


TSANTSAR SOYAYYA : Ita ce lokacin da Manzon Allah (saww) yaga Sahabinsa mai suna Thawbanu duk launin fuskarsa da jikinsa ya chanza. Sai ya tambayeshi "MENENE YA SAMEKA YA THAWBANU?".

Sai yace : "Ya Rasulallahi wallahi babu rashin lafiya ko Jinya tare dani. Sai dai ni idan ban ganka ba, ina shiga cikin wani mawuyacin hali. Har sai nazo na kalleka tukunna!".


TSANTSAR SOYAYYA : Ita ce lokacin da Abdullahi bn 'Ubayy bn Salul ya fadi bakar Magana akan Manzon Allah (saww) nan take sai 'Dansa ya zare takobi zai kasheshi..

Yace: "Kaine Makaskanci. Kuma idan ka maimaita abinda ka fada wallahi sai na kasheka!!".


TSANTSAR SOYAYYA : ita ce lokacin da Manzon Allah (saww) yace "KADA KU CHUTAR DANI ACIKIN LAMARIN A'ISHA". (Wato idan kuka chutar da ita, to ni kuka chutar).


TSANTSAR SOYAYYA : Ita ce lokacin da {MANZON ALLAH} {SAW} ya rika hannun Imam Hasan da Imam Husaini, sannan yace : "DUK WANDA YASO WADANNAN GUDA BIYUN NAN, SANNAN YASO MAHAIFINSU DA MAHAIFIYARSU, TO YANA TARE DANI AGIDAN ALJANNAH".

Kuma yace "Ya {ALLAH} ina son Alhusaini. Ya {ALLAH} kasoshi, kuma kaso duk mai sonsa".

{MANZON ALLAH} {SAW} yace  "MAFIYA SOYAYYATA ACIKIN AL'UMMATA, WASU MUTANE NE WADANDA ZASU ZO ABAYANA. 'DAYANSU ZAI YI BURIN YA BAYAR DA IYALANSA DA DUKIYARSA DOMIN YA SAMU GANINA".

Ya {ALLAH} kasa MU-NE!! Ya {ALLAH} kasa MU-NE!! Ya {ALLAH} kasa MU-NE!!.

Anan zamu tsaya sai wani karon kuma.. Zamu ci gaba

Ya Allah yi salati da aminci bisa {ANNABINMU MUHAMMADU} tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa da dukkan Masoyansa tare damu baki daya.

Kowa yayi forwarding don soyayyarsa da {MANZON RAHAMA

No comments:

Post a Comment